Shugaban Iran Masoud Pezeshkian ranar Lahadi ya yi gargaɗin cewa za su gwabza yaƙi da duk ƙasar da ta kuskura ta kai hari kan Shugaban Addini na ƙasar Ali Khamenei, a yayin da ake ci gaba da musayar yawu tsakanin Tehran da Washington kan zanga-zangar da ake yi a Iran.
Pezeshkian a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa X ya ce Duk wani hari da za a kai wa babban shugaban ƙasar su yana nufin ƙaddamar da gagarumin yaƙi kan ƙasar Iran.
Pezeshkian ya ɗora alhakin taɓarɓarewar tattalin arzikin Iran kan abin da ya bayyana a matsayin shekaru aru-aru da Amurka da ƙawayenta suka kwashe suna ƙaƙaba wa ƙasarsa takunkumai lamarin da ya jefa ‘yan ƙasar cikin matsanancin hali.
Ya yi wannan gargaɗi ne bayan shugaban Amurka Donald Trump a wata hira da ya yi da Politico, ya bayyana Khamenei a matsayin “mutum mara lafiya,” sannan ya ce Iran “ƙasa ce mafi muni da ake rayuwa,” inda ya ƙara da cewa ƙasar tana buƙatar sabbin shugabanni.
