
Hukumar DSS ta yi gargadin shirin kungiyar ISWAP na kai hari a wasu garuruwan jihohin Ondo da Kogi.
Wannan gargadin na kunshe ne a cikin takardar sirri mai kwanan wata 20 ga Oktoba, 2025, wacce aka aike wa kwamandan 32 Artillery Brigade na rundunar sojin kasar nan da ke Akure.
Takardar wacce daraktan tsaro na DSS a jihar Ondo, Hi Kana, ya sanya wa hannu, ta nuna cewa an samu sahihin bayanan sirri cewa ‘yan ta’addan na shirin kai hare-hare.
Hukumar ta ce ‘yan ta’addan sun fara gudanar da leƙen asiri a wadannan yankuna, tana kuma roƙon jami’an tsaro da su ƙara matakan tsaro domin hana asarar rayuka da dukiyoyi.
Wannan gargadi na zuwa shekaru uku bayan mummunan harin da aka kai Cocin Katolika na Sant. Francis a Owo, a watan Yunin 2022, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane sama da 40.