Majalisar Zartarwa ta Tarayya ƙarƙashin jagorancin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ta amince da ayyukan ginawa da gyaran manyan hanyoyi guda tara a faɗin kasar nan da kuɗinsu ya kai kusan naira biliyan 631.3.
Daga cikin ayyukan da aka amince da su akwai hanyar Bichi Ring Road a nan jihar Kano, da tsawon aikin ya kai kilomita 47 tare da gadar sama wato flyover, kuma kudin aikin ya kai naira biliyan 89.2.
Ministan Ayyuka, Sanata David Umahi, ne ya bayyana hakan a ranar Laraba yayin da yake yi wa manema labarai na fadar shugaban ƙasa karin bayani bayan kammala taron FEC, wanda Shugaba Tinubu ya jagoranta a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja.
A cewar ministan, ayyukan hanyoyin za su gudana a shiyyar kasar nan guda shida, domin bunƙasa harkokin tattalin arziki, sauƙaƙa zirga-zirga, inganta haɗin kai tsakanin al’ummomi da kuma haɗa manyan cibiyoyin kasuwanci.
Ya bayyana cewa amincewar ta nuna ƙudurin gwamnatin Shugaba Tinubu na magance matsalar lalacewar manyan hanyoyi a Najeriya da kuma inganta hanyoyin sufuri a faɗin ƙasar nan.
