Sarkin Kano Muhammadu Sanusi na II ya ce, bai dace tarayya ta ci gaba da ciyo bashi ba bayan ta cire tallafin man fetur ba.
Sarkin ya fadi hakan ne yayin da yake jawabi a taron Oxford Global Think Tank Leadership da aka ƙaddamar da wani littafi Abuja ranar Talata.
Tsohon Gwamnan Babban Bankin kasan kuma Masanin tattalin arziki ya kuma ce, cire tallafin man ya haifar da ƙaruwar kuɗaɗen shiga na gwamnati.
Sarkin ya yaba wa gwamnatin Tinubu kan cire tallafin man fetur da daidaita farashin musayar kuɗi, yana mai bayyana matakan a matsayin “masu raɗaɗi amma na wajibi.”
Ya kuma ya yi gargadin cewa, duk wannan matakan, ba za su yi tasiri ba idan ba’asa gaskiya da tsauraran matakai kan kashe kuɗin gwamnati ba.
