Tsohon Ministan Shari’a kuma Babban Lauyan Tarayya, Abubakar Malami (SAN), ya musanta rahotannin da ke ikirarin cewa an gano makamai a wasu gidaje da ake zargin mallakinsa ne.
A cikin wata sanarwa da hadiminsa kan harkokin yaɗa labarai, Mohammed Bello Doka, ya fitar a ranar Laraba, Malami ya ce babu wata hukuma ta tsaro da ta sanar da shi, iyalansa ko lauyoyinsa cewa an gano makamai a ko wane gida da ake dangantawa da shi.
Ya kuma musanta duk wata alaƙa da ta’addanci ko ɗaukar nauyin ta’addanci, yana cewa an yi zargin ne ba tare da ambaton wani mutum, ƙungiya, mu’amala ko sahihiyar hujja ba.
Sanarwar ta kuma nuna damuwa kan yadda tun bayan kama Malami da Hukumar Tsaron Farin Kaya DSS ta yi a ranar Litinin, aka hana shi ganin iyalansa da lauyoyinsa, lamarin da ya ce ya saɓa da dokokin ƙasar nan.
Malami ya buƙaci kafafen yaɗa labarai da su nuna ƙwarewa da ɗabi’ar aikin jarida ta hanyar bambance tsakanin zargi da gaskiya, tare da barin doka ta yi aikinta ba tare da tasiri ba.
