Mahukuntan Saudiyya sun aiwatar da hukuncin kisa kan wasu ’yan ƙasar Bangladesh biyu bisa laifin aikata lalata a cikin wani masallaci da ke birnin Makka.
Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida ta Saudiyya ce ta bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ta fitar ranar Laraba, inda ta bayyana sunayen waɗanda aka kashe a matsayin Nazrul Islam Abdul Basir da Siti Akhtar.
Sanarwar ta ce jami’an tsaro sun kama mutanen biyu bayan faruwar lamarin, inda daga bisani aka gudanar da bincike tare da gurfanar da su a gaban kotu.
A cewar ma’aikatar, kotun ta same su da laifi, ta kuma yanke musu hukuncin kisa bisa tsarin hukuncin Ta’azir, saboda girman laifin da suka aikata da kuma keta alfarmar masallaci.
Ta ƙara da cewa hukumomin shari’a sun tabbatar da hukuncin kafin samun umarnin sarauta na aiwatar da shi, bisa tanade-tanaden Shari’ar Musulunci.
Ma’aikatar ta ce an aiwatar da hukuncin kisan a yankin Makka ranar Laraba.
Haka kuma, ta jaddada ƙudirin gwamnatin Saudiyya na tabbatar da tsaro da adalci, tare da aiwatar da dokokin Shari’ar Musulunci kan waɗanda suka aikata laifukan da suka shafi keta alfarmar masallatai da mutuncin wasu.
Ma’aikatar ta kuma yi gargaɗin cewa duk wanda ya aikata irin wannan laifi zai fuskanci hukuncin da Shari’ar Musulunci ta tanada.
