Hakan biyo bayan fashewar tayar jirgin saman kamfanin a yayin sauka a filin jirgin saman Malam Aminu Kano dauke da fasinjoji 53.
Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Sama ta Najeriya NCAA ta Kasa ta dakatar da jiragen MaxAir tsawon wata uku don gudanar da bincike kan fashewar tayar jirgin lokacin da yake sauka a filin jiragen sama na Kano ranar Talata.
Wata sanarwa da NCAA ta wallafa a shafinta na X ta ce matakin zai fara aiki ne daga tsakiyar daren Juma’a 31 ga watan Janairu na 2025.
Hukumar ta ce, matakin zai bai wa kamfanin damar sake yin nazari kan yadda yake gudanar da ayyukansa.
Ta kuma ce, ita ma za ta yi bincike mai zurfi kan tsarin kula da lafiyar masu hawa jirgin da tsarin tafiyar da kamfanin da ma’aikata da jiragen kamfanin, har ma da yadda kamfanin ke hada-hadar kudaɗe don gano cewa ko kamfanin zai iya ci gaba da zirga-zirgar jiragen sama a kasar.
Sanarwar ta ce MaxAir zai ci gaba da aiki ne kawai idan masu bincike sun gamsu da sakamakon da suka samu bayan kammala binciken.