Dakarun rundunar Operation Hadin Kai sun samu nasarar kama wanda ake zargin dan kunar bakin wake ne a jihar Borno tare da kama kayan da ake shirin amfani da su wajen kera bama-bamai na gida.
An kama wanda ake zargin mai suna Abubakar Mustapha a ranar Litinin ta hannun dakarun bataliya ta 152 tare da hadin gwiwar sauran hukumomin tsaro, a garin Banki da ke Karamar Hukumar Bama a jihar.
Jami’in yada labarai na rundunar haɗin gwiwa da ke Arewa maso Gabas, Laftanar Kanar Sani Uba, ya ce an sami Mustapha da kayan da aka riga aka hada, wanda ke nuna shirin kai hari nan ba da jimawa ba.
A wani labarin kuma dakarun da ke bakin iyakar Najeriya da Kamaru sun kama mota ƙirar Peugeot dauke da buhunan taki na Uriya guda shida, wanda ake amfani da shi wajen kera bama-bamai na gida.
Rundunar ta takwas ta sojojin ta ce dakarun sun kwato bindigogin AK-47 guda 189, dubban harsasai, da wasu kayan laifuka, tare da ceto mutane 1,023 da aka yi garkuwa da su a yayin hare-haren da aka gudanar a jihohin Sokoto, Katsina, Kebbi da Zamfara.
