An Fara Kaɗa Ƙuri’a a Zaɓen Ƙananan Hukumomi na Borno, PDP Ta Janye Daga Takarar
An fara kaɗa ƙuri’a a zaɓen ƙananan hukumomi na Jihar Borno, inda ake zaɓen shugabannin ƙananan hukumomi 27 da kansiloli 312 a faɗin jihar.
Zaɓen ya fara ne da safiyar ranar Asabar a dukkanin ƙananan hukumomi 27 da kuma mazabu 312 na jihar.
- PDP ta nada shugabannin riƙon ƙwarya a wasu jihohi
- Ba Tinubu ne ya sauko da farashin kayan abinci ba – ADC
- Mu za mu kafa mulki a 2027 – Sabon Shugaban PDP
Jam’iyyun da ke zaɓen sun haɗa da jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Boot Party, Labour Party (LP), Peoples Redemption Party (PRP), New Nigeria Peoples Party (NNPP), da kuma Social Democratic Party (SDP).
Sai dai a ranar Juma’a, jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta sanar da janyewarta daga zaɓen, tana mai danganta hakan da abin da ta kira rashin amincewa da hukumar zaɓe da kuma tsadar kuɗin sayen fom ɗin nuna sha’awa da na tsayawa takara.
PDP ta zargi Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Jihar Borno (BOSIEC) da gaza ba jam’iyyun adawa hujjojin da za su tabbatar da sahihanci da adalcin zaɓen.
Da yake mayar da martani kan janyewar PDP, shugaban BOSIEC, Tahir Shettima, ya ce hukumar ba za ta tilasta wa kowace jam’iyya shiga zaɓen ba.
