Nijeriya da Saudiyya sun rattaba hannu kan sabuwar yarjejeniyar fahimtar juna ta shekaru biyar, don karfafa hadin gwiwar tsaro a tsakanin kasashen biyu.
Yarjejeniyar, wacce aka sanar a ranar Talata a cikin wata sanarwa da Ahmed Dan Wudil, Mataimaki na Musamman kan Yada Labarai ga karamin Ministan Tsaro, Bello Matawalle, ya fitar, ta bayyana cewa, hadin gwiwar ta shafi dabarun horar da sojoji, raba bayanan sirri, samar da tsaro, da ayyukan hadin gwiwa.
Najeriya ba ta cikin kasashen da muka hana Bizan Hajji – Saudiyya
An sanya hannu a yarjejeniyar ne a Birnin Riyadh na kasar Saudiya, ta hannun karamin Ministan Tsaro na, Bello Matawalle, da Dr. Khaleed Al-Biyari na Saudiyya, wacce ake sa ran yarjejeniyar za ta zama tsarin ci gaban tsaro mai dorewa a fadin kasashen biyu
