Ƙungiyar masu buƙata ta musamman ta ƙasa, ta amince da tazarcen Shugaba Bola Ahmed Tinubu da Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf a zango na 2, tare da alƙawarin samarwa Shugaba Tinubu ƙuri’u miliyan 5 daga jihohin arewacin Najeriya 19 a zaɓen shekarar 2027.
Shugaban ƙungiyar na ƙasa, Comrade Yarima Sulaiman Ibrahim ne ya bayyana hakan, a wani taro da aka gudanar a Kano domin nuna goyon baya ga sake zaɓen Tinubu da Gwamna Abba.
Sulaiman ya ce goyon bayan Shugabannin biyu, matsaya ce da ƙungiyar da wakilan mambobinta daga jihohin arewa 19 suka amince da ita, yana mai cewa suna ganin jam’iyyar APC ta cika alkawuran da ta ɗauka a lokacin yaƙin neman zaɓe.
Da take jawabi a madadin Gwamna Abba Kabir Yusuf, Kwamishiniyar harkokin mata ta Kano, Hajiya Amina Abdullahi HOD, ta ce gwamnatin jihar na baiwa walwala da shigar masu nakasa cikin harkokin al’umma muhimmanci, ta yadda suke iya taka muhimmiyar rawa wajen ci gaban Kano da Najeriya baki ɗaya.
Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya rawaito shugaban ƙungiyar masu bukatar ta musamman na Kano, Sa’adu Ibrahim Gezawa, na tabbatar da cewa su da iyalan su daga jihohin arewacin Najeriya 19, da makusantansu, za su shiga zaɓen 2027 domin goyon bayan waɗanda ƙungiyar ta amince da su.
