
Matatar mai ta Dangote za ta fara fitar da tataccen man fetur zuwa nahiyar Asia a karon farko tun bayan da ta fara aiki.
Wata majiya daga cikin kamfanin ta bayyana cewa wani jirgin ruwa mai ɗauke da tan dubu 90 na fetur, mallakin kamfanin Mercuria, zai tashi zuwa Asiya a ranar Lahadi mai zuwa.
Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya rawaito cewa jigilar na nuna sabon salo a kasuwancin man Najeriya, wanda ke ƙara matsayi wajen samar da man da duniya ke bukata.
Daraktan kamfanin Horizon Engage, Mr. Clementine Wallop, ya bayyana wannan ci gaba a matsayin matakin tarihi da zai ba Najeriya damar zama abar dogaro a harkar samar da mai da tattalin arzikin fetur a duniya.
Tun bayan da matatar mai mai ƙarfin tace ganga 650,000 na ɗanyen mai a rana ta fara fitar da fetur a shekarar da ta gabata, ana fi jigilar man ne zuwa kasashen Yammacin Afirka.
Wannan sabuwar fitar da za ta nufi Asiya na nuna ci gaban kasuwancin fetur daga Najeriya zuwa kasuwannin duniya.