Saurari premier Radio
23.1 C
Kano
Sunday, September 22, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabarai'Yan jaridu na da gudumuwar da zasu kawo wanda iya kawo gagarumin...

‘Yan jaridu na da gudumuwar da zasu kawo wanda iya kawo gagarumin sauyi a nahiyar Afrika ta fuskar cigaba

Date:

Premier Radio na halartar babban taron muhawarar karo na farko akan zaman lafiya da hadin kai da kwanciyar hankali ta hanyar harshen Hausa tare da tabbatar da ‘yancin kan kasashen Afirka.

Taron dai na guda ne bisa Jagorancin shugaban ‘kasa kuma shugaban majalissar ceton Nijar a babban dakin taro na Æ™asa da Æ™asa na Muhatma Gandhi dake birnin Niamey a Jamhuriyar Nijar.

Taron dai ya zo ne a wani bangare na kafa kungiyar hadin kan yan jarida na kasashen Africa masu amfani da harshen Hausa domin ganin aikin jarida ya kawo sauyi ga yankin.

Masu jawabai sun mayar da hankali kan irin rawar da Yan jaridu zasu taka wajen kawo sauyi da cigaba mai dorewa ta hanyar sauke hakkokin da Yan jarida ke dasu wajen fadin gaskiya komai dacinta.

Jigon taron shine gudunmuwar da yan jaridu zasu bayar wajen ingata zaman lafiya da hadin kai da kuma kwanciyar hankali ta hanyar harshen hausa tare da tabbatar da yancin kan kasashen Africa

Taron dai ya samu halartar wasu daga cikin Yan Najeriya da suka hadar da Major Hamza Almustapha da Hajiya Naja’atu Muhammad da kuma wasu daga cikin Sarakunan gargajiya da suka hada da Sarkin Machina da Sarkin Tunga Sarkin Talata-Mafara da dai sauransu.

Latest stories

Related stories

Tinubu ya gana da Sarki Charles III a fadar Buckingham

Shugaban kasa Bola Tinubu ya yi wata ganawar sirri...

PDP ta ki sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya a zaben gwamnan jihar Edo

Jam’iyyar PDP ta ki sanya hannu kan yarjejeniyar zaman...