Shugaban kasa Bola Tinubu ya bayar da umarnin a gaggauta bude cibiyar bayar da agajin gaggawa ta kasa a jihar Neja,biyo bayan mummunar ambaliyar ruwa da ta afku a karamar hukumar Mokwa ta jihar.
Shugaban ya bayar da wannan umarni ne da sanyin safiyar Asabar din nan bayan da rahotanni suka nuna cewa ambaliyar ta yi sanadin asarar rayuka sama da 100 tare da raba iyalai da dama.
A wata sanarwa da ya fitar a shafin sa na X, Shugaba Tinubu ya yi jimamin faruwar ibtila’in, ya kuma yi alkawarin daukar matakin gaggawa da tura agajin jin kai na gwamnatin tarayya don tallafa wa al’ummomin da abin ya shafa.
