
An kashe wani makiyayi da kuma shanu fiye 100 a jerin wasu hare-haren da aka kai kan makiyaya a ƙauyuka biyu da ke cikin Kananan Hukumomin Jos ta Kudu da Jos ta Arewa a Jihar Filato.
Hare-haren, wanda ake zargin wasu ’yan bindiga ne suka kai ta hanyar buɗe wuta kan makiyayan, sun sake jaddada yadda tsaro ya taɓarɓare a yankunan da ke fama da rikice-rikice tsakanin manoma da makiyaya, wanda a kullum ke janyo asarar rayuka da dukiyoyi.
Sakataren ƙungiyar Miyetti Allah (MACBAN) reshen jihar, Ibrahim Yusuf Babayo, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya zargi matasa ‘yan kabilar Berom daga ƙauyukan da abin ya shafa da hannu a hare-haren.
Sai dai shugabancin ƙungiyar matasan Berom ya musanta zargin, inda suka bayyana shi a matsayin farfaganda kawai.
Rahotanni sunce harin farko ya faru ne da yammacin Talata a kauyen Gero da ke Jos ta Kudu, yayin da na biyu ya faru da safiyar Laraba a kauyen Darwat da ke cikin ƙaramar hukumar Riyom.
A cewar Babayo, makiyaya uku sun jikkata a harin da aka kai a Gero inda ɗaya daga cikinsu yake karɓar magani a asibiti da ke Jos, yayin da sauran biyun ke jinya a asibitin Sojoji na Rukuba Barracks, Jos.