
Shugaban Amurka Donald Trump, ya ƙi bayyana cikakken matsayinsa kan ƙasar za ta shiga rikicin da ke ƙara tsananta tsakanin Iran da Isra’ila, yayin da ake shiga rana ta bakwai a jere da kasashen biyu na kai wa juna hare-hare.
Shugaban ya furta hakana ne a tattaunawarsa da ‘yan jaridu a ranar Laraba a Fadar White House.
“Wataƙila mu shiga, wataƙila kuma ba za mu shiga ba.
“Gwamnatin Iran ta nemi damar ganawa da ni a Fadar White House, amma na ƙi amincewa… kamata ya yi Iran ta nemi hakan tun da farko kafin ƙarfin ta ya ƙare. In ji shi.
A Iran kuwa, Jagoran Addinin ƙasar, Ayatollah Ali Khamenei, ya fitar da gargaɗi mai ƙarfi kan tsoma bankin wata kasa a fadan, yana mai cewa, Iran za ta mayar da martani cikin ƙarfin hali idan Amurka ta kusakura ta ɗauki matakin soji a kanta.
Tashin hankali dai na ci gaba da ruruwa a yankin, yayin da kasashen duniya ke ci gaba da bibiyar lamarin cikin fargaba da sa ido kan matakin da manyan ƙasashe za su ɗauka.