
Iyalan Marigayi Bilyaminu Bello wanda matarsa Maryam Sanda ta hallaka kuma kotun Koli ta tabbatar hukuncin kisa a kanta sun yi martani ga afuwar da shugaban kasa Bola Tinubu ya yi mata.
Dakta Bello Muhammad ya kalubalanaci afuwar da kuma sakinta a cikin wata sanarwa da ya fitar a madadin iyalan marigayin a ranar Litinin.
“Bai kamata shugaba Tinubu ya hada da Maryam Sanda cikin masu laifin da ya yiwa afuwa ba, saboda hakan tamkar fami ne kan raunin da muka fara warkewa daga gare shi.
“Yin wannan afuwa ga Maryam Sanda rashi adalci ne garemu.” In ji sanarwar.
Dangin nata sun kammala da cewa sun bar komai ga adalcin Allah, “Mai Shari’a na gaskiya,” tare da yin addu’a ga Allah Ya jikan Bilyaminu, Ya kuma ba ’ya’yansa da masoyansa ƙarfin jure wannan raɗaɗin.
A watan Disambar 2020, Mai Shari’a Yusuf Halilu, na Kotun Ɗaukaka Ƙara ya yanke mata hukuncin kisa ta hanyar rataya, wanda daga baya Kotun Koli ta tabbatar a watan Oktoba 2023.
Daga lokacin zuwa yanzu Maryam ta yi zaman shekara shida da wata takwas a Babban Gidan Yarin Suleja.