Shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu ya yaba da nasarar ceto dalibai 100 na makarantar St. Mary’s da ke Jihar Naija daga hannun ’yan bindiga.
Mai magana da yawun shugaban kasa, Bayo Onanuga, ne ya bayyana hakan a daren jiya Litinin.
A cewarsa, shugaban kasan ya umarci hukumomin tsaro da su gaggauta kubutar da sauran dalibai 115 da ke hannun ’yan bindigar.
Gwamnatin tarayya, tare da gwamnatin Jihar Naija, na aiki domin ganin an mika yaran da aka ceto ga iyayensu cikin koshin lafiya, tare da ƙara tsaro a makarantun jihar.
Daliban 100 sun isa gidan gwamnati a daren Litinin, duk da cewa har yanzu babu bayani tabbatacce kan ko an biya kudin fansa ko a’a.
’Yan bindigar sun kai harin makarantar ne a ranar 21 ga Nuwamba, 2025, inda suka sace mutane 315, dalibai 303 da malamai 12.
