
Shugaba Tinubu ya karrama ‘yan wasan kwallon kafa mata ta Najeriya, Super Falcons da tukwicin kuɗi sama da naira miliyan 150 da kuma gidaje bayan samun nasararsu na lashe gasar cin kofin ƙwallon ƙafa ta mata ta Afirka (WAFCON) karo na goma.
Shugaban ya ba kowacce ‘yar wasa gida mai ɗaki uku, yayin da mai horas da su tawagar kyautar kuɗi sama da naira miliyan 75.
Hakan ya faru ne a taron na karramawa ta musamman da ya gudana a fadar gwamnatin tarayya a Abuja a ranar Litinin, shugaba Tinubu ya kuma ya yabawa gwanintar da jajircewar ‘yan wasan wanda ya kai su ga nasarar lashe kofin da aka gudanar a ƙasar Morocco.