Gwamnan Jihar Anambra, Farfesa Chukwuma Charles Soludo, ya bayyana cewa Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ba ya bukatar yin maguɗin zaɓe domin samun nasarar sake lashe zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2027.
Soludo ya bayyana hakan ne yayin wani gangamin siyasa da aka gudanar a dandalin Alex Ekwueme Square da ke Awka, babban birnin Jihar Anambra, inda ya nuna kwarin gwiwarsa kan damar da jam’iyyar APC mai mulki take da ita na lashe zaɓen mai zuwa.
Gwamnan ya yi ikirarin cewa Tinubu da mataimakinsa, Sanata Kashim Shettima, suna da isasshen ƙarfin siyasa da goyon bayan jama’a a faɗin ƙasar da za su iya kai su ga nasara ba tare da amfani da maguɗin zaɓe ba.
A cewarsa, jam’iyyun adawa ba su da ƙarfin tasiri a dukkan sassan Najeriya, inda ya yi zargin cewa wasu daga cikin ‘yan takararsu suna samun goyon baya ne kawai a wasu yankuna na ƙasar.
Soludo ya kuma bayyana cewa ayyukan da gwamnatin Tinubu ta gudanar tun bayan hawanta mulki za su taka muhimmiyar rawa wajen tantance sakamakon zaɓen 2027.
Haka kuma, gwamnan ya kare wasu daga cikin manufofin gwamnatin tarayya, musamman sauye-sauyen tattalin arziki, matakan tsaro da shirin tallafin karatun ɗalibai na NELFUND.
