Kasar Syria ta ayyana tsagaita wuta na tsawon kwanaki hudu a rikicin da ke gudana tsakanin sojojin kasar da mayakan Kurdawa masu fafutukar neman ‘yancin yankinsu.
A cikin wata sanarwa da ta fitar, gwamnatin Syria ta bayyana cewa idan aka mutunta yarjejeniyar dakatar da bude wuta, sojojin kasar ba za su sake kai farmaki ko shiga manyan biranen kasar ba.
Hakazalika, kasar Syria ta bukaci kungiyar mayakan SDF da su gabatar da sunayen mutanen da za a nada a matsayin manyan jami’an gwamnati, ciki har da mukaman da suka shafi harkokin tsaro, kamar mataimaki na musamman ga Ministan Tsaro.
Gwamnatin ta ce wannan na daga cikin kokarinta na hada mayakan Kurdawa cikin tsarin tafiyar da harkokin gwamnati.
Gwamnatin Syria ta kuma bayyana aniyarta ta bude kofar siyasa ga Kurdawa, tare da ci gaba da tattaunawa domin tabbatar da zaman lafiya mai dorewa.
Ta jaddada muhimmancin tsayawa kan yarjejeniyar da aka cimma a ranar 18 ga watan Janairu, wadda ta bukaci daukar matakin dakatar da yaduwar rikicin da ke tsakanin sojojin kasar da ‘yan tawayen Kurdawa.
