
Rundunar sojin Isra’ila ta bayyana cewa dakarunta biyar sun mutu yayin da wasu biyu suka ji rauni a wani faɗa da ya ɓarke a arewacin Zirin Gaza, musamman a yankin Beit Hanoun.
Rahotanni daga kafofin yaɗa labaran Isra’ila sun ce, lamarin ya faru ne sakamakon fashewar wasu bama-bamai da aka dasa a gefen hanya, wanda ya auka wa motocin sojojin yayin da suke gudanar da aiki a yankin.
Kakakin ƙungiyar Hamas ya tabbatar da cewa mayaƙan ƙungiyar sun kai harin ga sojojin Isra’ila a yankin da ya shahara da rikice-rikice da sarƙaƙiya.
Sai dai har yanzu babu cikakken bayani daga bangarorin biyu kan adadin asarar da aka tafka.
Wannan hari na baya-bayan nan na zuwa ne kasa da wata guda bayan da Isra’ila ta rasa dakarunta bakwai a kudancin Gaza, mafi muni tun bayan barkewar sabon rikici da ƙungiyar Hamas a Gaza.