Dakarun sojin ƙasar nan sun kai samame a yankin Faruruwa, kusa da kauyukan Goron Dutse da Tsaure a ƙaramar hukumar Shanono, a daren Asabar, inda suka halaka ‘yan bindiga da dama tare da kama wasu.
A yayin sumamen sojojin sun kwato babura kusan 30 da ake amfani da su wajen kai hare-hare a yankunan karkara.
Samamen ya kasance na ci gaba da yaki da ‘yan bindiga a arewacin Kano, wanda ya haɗa da sintiri da kuma fatattakar yan Ta’adan da ke ɓoye a dazuzzuka.
Sai dai a yayin arangamar, sojojin sun yi rashi, inda aka tabbatar da mutuwar soja ɗaya.
Nasarar sojojin na zuwa ne bayan da suka sami rahoton afkawar ƴan bindigar wasu ƙauyukan yankin inda suka yi yunƙurin tafiya da ɗaruruwan dabbbobi sai dai sojojin sun rutsasu inda sukai masu fata fata.
Shugaban ƙaramar hukumar Shanono Hon. Abubakar Barau ya yaba da namijinƙoƙarin jamian tsaron tare da yin alƙawarin cigaba da basu dukkan irin gudummawar da suke buƙata ta kowacce fuska.
Shaugaban ƙaramar hukumar ta Shanono ya godewa gwamnatin jiha data tarayya bisa yadda take ƙoƙari babu dare ba rana domin ganin an kakkaɓe ƴan bindigar dake kutsawa yankin na Shanono.
Tuni dai aka tura ƙarin dakarun ƙasa da na sama domin ci gaba da aiki a yankin da kewaye, da nufin tabbatar da cewa ba a bai wa ‘yan bindigar damar sake komawa ba.
