Rundunar Sojin Nijeriya ta bayyana cewa dakarunta na Operation WHIRL STROKE (OPWS) sun gano wata masana’antar ƙera makamai ba bisa ƙa’ida ba da ke ɓoye a yankin Agwatashi, cikin ƙaramar hukumar Doma ta Jihar Nasarawa.
A cewar rundunar, an gano wurin ne yayin da sojoji ke gudanar da aikinsu na sintiri domin hana masu aikata laifuka yin kutse da samun ‘yancin motsi a yankin.
Wannan bayani ya fito ne a cikin wata sanarwa da rundunar ta wallafa a shafinta na X.
Rahotanni sun nuna cewa an ɓoye wurin ne domin ƙera makamai da ake bai wa masu aikata laifuka a yankin da ma kewaye.
Binciken da sojoji suka gudanar a wurin ya haifar da gano bindigogi guda shida da aka ƙera, tare da kayan aiki da na’urorin ƙera makamai.
Haka kuma, an kwato kuɗi da wayar salula daga hannun wani mutum da aka kama a wurin.
Kwamandan rundunar, Manjo Janar Moses Gara, ya jaddada muhimmancin dogaro da sahihan bayanan sirri, inda ya buƙaci dakarun su ci gaba da amfani da ingantaccen bayanan leƙen asiri domin tarwatsa cibiyoyin aikata laifuka da dakile barazanar tsaro a yankin.
