Sojoji ƙarƙashin dakarun haɗin gwiwa na JTF sun ƙwato dabbobi 257 bayan daƙile wani harin ɓarayin shanu a ƙaramar hukumar Gwarzo a nan Kano.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Mataimakin Daraktan Hulɗa da Jama’a na rundunar Manjo Babatunde Zubairu ya fitar a ranar Litinin.
“Lamarin ya faru ne da sanyin safiyar Lahadi karkashin dakarun sojin ƙasa na Rundunar 3 Brigade daga sansaninsu da ke Gwarzo.
“Dakarun sun amsa kiran gaggawa da misalin ƙarfe 6:57 na safe, inda suka yi saurin kai ɗauki zuwa wata hanyar da ake zargin ’yan bindiga ke bi.
“Sojojin sun yi wa wata ’yan bindiga kwanton ɓauna, sun kuma fafata da su a ƙauyen Dayi, waɗanda tun da farko aka samu rahoton sun sato dabbobi daga ƙauyen Mainika a cikin Gwarzo”. In ji sanarwar.
Dabbobin da aka ƙwato sun haɗa da shanu 135 da tumaki 119 da akuya guda ɗaya da kuma jakuna biyu, wanda jimillarsu ta kai 257.
Mahukuntan sun tabbatar da cewa an miƙa dabbobin ga masu su ta hannun shugabannin al’umma da na ƙananan hukumomi.
