Dakarun Operation Hadin Kai da ke yaƙi da ta’addanci a shiyar Arewa maso Gabashin kasar nan, sun daƙile wani harin da mayaƙan ƙungiyar ISWAP suka kai a wani sansanin sojoji da ke garin Mairari a jihar Borno, inda suka kashe ƴan ta’adda da dama.
Da yake tabbatar da harin a wata sanarwa da ya fitar a karshen mako, jami’in yaɗa labarai na rundunar Laftanar Kanar Sani Uba, ya ce ƴan ta’addar sun yi yunkurin kutsawa sansanin ne ta hanyar amfani da wasu ababen fashewa.
Sai dai ya ce dakarun ba tare da wani lokaci ba, sun samu nasarar gano ababen fashewar tare da warwaresu, wanda hakan ya dakatar da kai harin cikin sansanin sojin.
Kanar Sani Uba ya ce dakarun sojin sun kuma samu nasarar kwace wasu kayayyaki daga wajen ƴan ta’addan da suka hada da bindiga ƙirar AK-47 da aburusai da gurneti da babura da na’urorin sadarwa da dai sauransu.
Yankin Arewa maso Gabashin Najeriya na ya daɗe yana fama da hare-haren ƴan ta’adda, wanda ke haifar da asarar rayuka daga ɓangaren fararen hula da kuma jami’an tsaro.
