Sojoji ƙarƙashin dakarun haɗin gwiwa na JTF sun ƙwato dabbobi 257 bayan daƙile wani harin ɓarayin shanu a ƙaramar hukumar Gwarzo a nan Kano.
Aikin, wanda dakarun sojin ƙasa na Rundunar 3 Brigade ke jagoranta daga sansaninsu da ke Gwarzo, ya gudana ne da sanyin safiyar ranar Lahadi, 1 ga Maris, 2026.
Wata sanarwa da Mataimakin Daraktan Hulɗa da Jama’a na rundunar Manjo Babatunde Zubairu, ya fitar, ta ce dakarun sun amsa kiran gaggawa da misalin ƙarfe 6:57 na safe, inda suka yi saurin kai ɗauki zuwa wata hanyar da ake zargin ’yan bindiga ke bi.
Sanarwar ta bayyana cewa dakarun sun yi wa wata ƙungiyar ’yan bindiga kwanton ɓauna da suka fafata da su a ƙauyen Dayi, waɗanda tun da farko aka samu rahoton sun sato dabbobi daga ƙauyen Mainika a cikin Gwarzo.
Bayanai sun ce dabbobin da aka ƙwato sun haɗa da shanu 135, tumaki 119, akuya guda ɗaya da jakuna biyu, wanda jimillarsu ta kai 257.
Mahukuntan sun tabbatar da cewa an miƙa dabbobin ga masu su ta hannun shugabannin al’umma da na ƙananan hukumomi, yayin da aka ce ’yan bindigar sun tafka asara mai yawa a yayin fafatawar.
