Shugaban Ƙasar Turkiyya, Recep Tayyip Erdogan, ya jaddada ƙudirin ƙasarsa na saka jarin da ya kai dala biliyan 5 a fannin kasuwanci da Najeriya.
Shugaba Erdogan ya bayyana hakan ne a ranar Talata a Ankara, yayin taron manema labarai na haɗin gwiwa da Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, a yayin ziyarar aiki ta Shugaban Najeriya zuwa Turkiyya.
Shugaba Erdogan ya ce an soma tattaunawa kan cimma wannan buri, tare da amincewa da kafa Kwamitin Haɗin Gwiwar Tattalin Arziki da Kasuwanci tsakanin ƙasashen biyu, domin faɗaɗa damar kasuwanci da ƙarfafa zuba jarin ‘yan kasuwar Turkiyya a Najeriya.
- Tinubu Ya Amince da Tura Sabbin Jakadu Hudu zuwa Faransa, Amurka, Birtaniya da Turkiyya
- Mambobin Kwamiti Sun Rubuta wa Tinubu, Ana Neman Shugaban Hukumar Nahcon Ya Yi Murabus
Ya yaba da jajircewa da ƙudirin Shugaba Tinubu wajen jawo zuba jari, yana mai cewa halartar ministoci da manyan jami’ai daga Najeriya wata bayyananniyar shaida ta wannan aniya.
Shugaba Erdogan ya yaba da sauye-sauyen da Shugaba Tinubu ke jagoranta a fannin makamashi, wanda ya taimaka wajen sake fasalin tattalin arzikin Nijeriya. Ya kuma yi fatan cewa haɗin gwiwar Kamfanin Man Fetur na Turkiyya (TPAO) da abokan aikinsa a Najeriya zai haifar da sakamako mai kyau.
A nasa jawabin, Shugaba Tinubu ya nuna godiya ga Turkiyya kan buɗaɗɗiyar zuciya da shirinta na haɗin gwiwa domin ƙarfafa ‘yanci, zaman lafiya da walwala a duniya. Ya jaddada muhimmancin gina tattalin arziki da ya haɗa kowa da kowa, musamman masu rauni.
