Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya faɗaɗa jadawalin kamfen ɗinsa na neman wa’adi na biyu a zaɓen 2027, inda aka ƙara yawan jihohin da zai ziyarta daga 12 zuwa 19, tare da cire Bauchi daga jerin wuraren da zai halarta da kansa.
A sabon jadawalin da aka bayyana, Tinubu zai halarci tarukan kamfen guda 20, ciki har da Abuja, tsakanin 24 ga Oktoban 2026 da 13 ga Janairun 2027.
Jihohin da aka ƙara sun haɗa da Katsina, Taraba, Zamfara, Imo da Kwara, baya ga Akwa Ibom, Jigawa da Kebbi da ya riga ya ziyarta.
A cewar jadawalin, shugaban zai gudanar da kamfen a Katsina ranar 2 ga Disamba, Kano ranar 17 ga Disamba, Taraba ranar 19 ga Disamba, Zamfara ranar 28 ga Disamba, da Imo ranar 30 ga Disamba.
A shekarar 2027 kuma, zai ziyarci Adamawa, Sokoto, Kwara da Delta, kafin kammala kamfen ɗinsa da babban taro a Legas ranar 13 ga Janairu.
Duk da cewa jam’iyyar APC ta tsara tarukan kamfen 37 a jihohi 36 da Abuja, Tinubu zai halarci guda 20 ne da kansa, yayin da wasu shugabannin jam’iyyar za su jagoranci sauran.
Tun da farko, Tinubu ya bayyana cewa ba zai iya halartar dukkan tarukan ba saboda nauyin gudanar da mulki da sauran buƙatun ƙasa.
Matakin ya jawo suka daga wasu ’yan adawa, ciki har da Adewole Adebayo na SDP da ƙungiyar Peter Obi Media Reach, waɗanda suka ce ya kamata shugaban ya gana da ’yan Najeriya domin amsa tambayoyi kan ayyukan gwamnatinsa.
Sai dai APC ta kare matakin, tana mai cewa babu wata doka da ta wajabta wa ɗan takarar shugaban ƙasa ziyartar dukkan jihohin Najeriya kafin zaɓe.
