Sojojin Najeriya ta ce ta yi nasarar ceto matar wani tsohon Birgediya Janar da wasu ’yan bindiga suka yi garkuwa da ita daga gidanta da ke Abuja a ranar 1 ga Satumba, 2026.
Rundunar ta ce an ceto matar ne bayan dakarun Guards Brigade da Army Headquarters Garrison sun ƙaddamar da wani samame na haɗin gwiwa domin bin sawun masu garkuwa da mutanen da kuma kubutar da wanda aka sace.
A cewar rundunar, dakarun sun samu sahihan bayanan sirri da suka kai su yankin Aco Estate zuwa Goza Community, inda suka yi arangama da masu garkuwa da mutanen.
Rundunar ta ce yayin musayar wuta da masu garkuwa da mutanen lamarin da ya tilasta musu barin matar da suka yi garkuwa da ita tare da tserewa.
Daga bisani, an samu nasarar ceto matar a ƙauyen Angwan Sabo, yayin da dakarun suka ci gaba da bin sawun waɗanda ake zargin.
