Atiku Abubakar 2011 President campaign Photo by www.mortenfauerby.dk ©mortenfauerby 2010 - all rights reserved
Wani tsagi na jam’iyyar ADC a jihar Adamawa ya dakatar da tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, bisa zargin haddasa rashin haɗin kai a jam’iyyar.
Tsagin ya kuma dakatar da tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya, Babachir Lawal da shugaban kwamitin riƙon kwarya na jam’iyyar, Sadiq Ibrahim.
Shugaban wannan tsagi na ADC a Adamawa, Raji Zumo, ne ya sanar da hakan yayin taron manema labarai da ya gudanar a Yola.
Ya ce an ɗauki matakin ne saboda rawar da suka taka wajen haddasa rabuwar kai, kafa tsarin shugabanci na daban da kuma saba wa umarnin kotu.
Tun bayan da gamayyar yan adawa suka karɓi shugabancin ADC a watan Yulin 2025, jam’iyyar ke fama da rikicin cikin gida.
A baya, tsohon mataimakin shugaban jam’iyyar na ƙasa, Nafiu Bala, ya kalubalanci sahihancin shugabancin David Mark, yana zargin an naɗa shi ba bisa ƙa’ida ba.
A ranar 1 ga Afrilu, hukumar zaɓe ta ƙasa ta dakatar da amincewa da ɓangaren David Mark, bisa umarnin wucin gadi na kotun ɗaukaka ƙara.
Yanzu dai kotun koli ta sanya ranar Talata domin sauraron ƙarar da David Mark ya ɗaukaka kan shari’ar da Nafiu Bala ya shigar, wadda ke ƙalubalantar shugabancinsa.
