Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid na shirye – shiryen dawo da tsosho kyaftin dinta Sergion Ramos daga Sevilla domin maye gurbin Brazil Eder Militao, mai shekara 26 wanda ya tafi doguwar jinya.
Hakan na zuwa ne bayan da Eder Militao mai buga mata baya ya samu rauni a wasan da kungiyar ta cinye Osasuna da ci Hudu da nema a gasar Laliga.
Jami’an Real Madrid na ganin cewa Ramos zai iya maye gurbin Militao a matakin na baya.
Rashin Dani Carvajal da Alaba da Tchoumeni kef da ke fama da rauni a kungiyar ya haifar mata da koma baya a fafatwar da take yi.
Sergio Ramos dan shekara 38 a da, shi ne kyaftin din kungiyar.