
Kwamishinanan Yada Labarai Ibrahim Abdullahi Wayya ne ya yi buda baki da matasan ya kuma yi alkawarin tallafawa rayuwarsu
Gwammatin jihar Kano ta ce, za ta ci gaba da tallafawa rayuwar mutanan da suka tuba suka daina aikata laifin Daba a karkashin shirinta na Safe Corridor wato tudun mun tsira
Kwamishinan yada labarai Kwamred Ibrahim Abdullahi Waiya ne ya bayyana hakan a jawabinsa lokacin da yake shan ruwa da yan daban da suka tuba suka daina aikata daba a karkashin shirin na Safe Corridor.
“Kofa a bude take ga duk wani mutum dake aikata wani laifi da zai tayar da hankalin mutane na ya tuba ya daina”

Wasu daga cikin mutanen da sun bayyana jin dadinsu tare da sake jaddada kudurinsu na daina aikata ayyukan Daba da kuma jawo wadan da keyi dan su tu ba su daina.
Gwamnatin jihar Kano dai ta ce za ta cibgaba da fito da hanyoyi da dama da za su dakile aikata ayyukan Daba da shaye-shaye a fadin jihar.