
Aminu Abdullahi Ibrahim
Hukumar jin daɗin alhazai ta jihar Kano ta sake jaddada cewa 25 ga Satumba, 2026 ita ce ranar ƙarshe da masu niyyar zuwa aikin Hajjin 2027 za su biya kuɗin ajiya tare da kammala rajista.
Babban Daraktan hukumar, Abubakar Ibrahim Matawalle, ya bayyana hakan ne yayin ganawa da jami’an cibiyoyin aikin Hajji na ƙananan hukumomi 44 a zauren taro na hukumar.
Ya tunatar da mahalarta taron cewa hukumar ta riga ta ayyana Naira miliyan 8 a matsayin kuɗin ajiya na aikin Hajjin 2027, tare da sanya 25 ga Satumba, 2026 a matsayin ranar rufe rajista.
Matawalle ya buƙaci duk masu niyyar zuwa aikin Hajji da su gaggauta kammala biyan kuɗin ajiya da rajista kafin wa’adin ya cika domin tabbatar da samun gurbin zuwa Hajji.
Ya kuma jaddada cewa ba za a ƙara wa’adin rajista ba, kuma ba za a ba kowa gurbin Hajji ba bayan ranar rufe rajista.
Hukumar ta ce za ta ci gaba da tabbatar da gudanar da aikin Hajji cikin tsari, gaskiya da inganci, tare da ƙarfafawa masu neman zuwa Hajji su cika dukkan ka’idojin rajista kafin wa’adin ya ƙare.
