Sanarwar dakatarwar da ta fara aiki nan take ta ce an ɗauki matakin ne domin bai wa gwamnati damar gudanar da cikakken bincike kan zarge-zargen da ake yi wa jami’in
A yayin da ake gudanar da binciken, an umarci babban daraktan da ya fi kowa girma a hukumar da ya karɓi ragamar gudanar da ayyukanta, domin tabbatar da cewa ayyukan hukumar ba su samu tangarda ba
Gwamna Fintiri ya ce matakin wani ɓangare ne na ƙoƙarin gwamnatinsa na tsaftace da sake fasalin fannin ilimi domin inganta ayyukan ilimi a jihar
Ya kuma jaddada cewa gwamnatinsa za ta ɗauki matakan da suka dace domin kare martabar tsarin ilimi, tare da gargadin jami’an gwamnati da masu riƙe da mukamai da su mutunta ƙa’idojin gudanar da aiki, gaskiya da rikon amana
