Pillars ta raba maki da Heartland a Sani Abacha
Ahmad Hamisu Gwale
Kungiyar Kwallon kafa ta Kano Pillars, ta gaza samun maki uku a wasan da ta fafata da Heartland a filin wasa na Sani Abacha da ke Kofar Mata, a wasa mako na 12 a gasar Firimiyar Najeriya.
Heartland ce ta fara zura kwallo a ragar Pillars ta hannun dan wasa Surajo Lawan a minti na 51, kuma ya kara ta biyu ta minti na 59.
Daga bangaren Pillars kuwa, Ahmad Musa da Rabiu Ali ne suka zura kwallo biyun a minti na 57, da minti na 75.
Karon farko kenan da Pillars ke buga wasa a Kano a gasar ta Firimiyar Najeriya, bayan ta koma Katsina da buga wasannin gida.
Kawo yanzu haka, Kano Pillars na mataki na 6 da maki 18 a wasanni 12 da ta fafata, kuma zata ziyarci Lobi Stars a wasa mako na 13 da zasu kece raini a mako mai zuwa.
An samu cikowar magoya baya da alkaluma suka nuna akalla mutane Dubu 15 sun ziyarci filin wasa na Sani Abacha domin kallon wasan na Kano Pillars.
Kano Pillars na karkashin jagoranci Usman Abdallah, da yake fatan lashe gasar Firimiyar Najeriya a karon farko da kungiyar tun kakar wasannin shekarar 2024.