Wani rahoton 2026 da Jami’ar City University dake Paris ɗin ƙasar Faransa ta fitar, ya ce binciken da ta gudanar a tsakanin jihohi 209 na yankin Sahel dake Afrika, ya sanya Kano a mataki na farko wajen kashe kuɗi a fannin ilimi, kuma ta biyu a harkokin kula da sauyin yanayi.
Jami’ar ta bayyana hakan ne a wajen wani taro da ta shirya, domin baiwa Kano kyaututtuka biyu bisa irin nasarar da ta samu a fannin samar da kuɗaɗen ilimi da kuma shugabanci a harkar sauyin yanayi.
Da take gabatar da kyautur Daraktar jami’ar ta City University dake Paris, Farfesa Julie Peghini, tare da abokin bincikenta Dr Hicham Tojari, sun ce Kano ce ta zo ta farko wajen kashe kuɗaɗen ilimi, sannan ta biyu wajen kula da sauyin yanayi cikin gwamnatocin jihohi 209 da aka tantance.
Wakiliyar Najeriya a UNESCO da ke Faransa, Dr Hajjo Sani, ta yabawa Gwamna Abba Kabir Yusuf bisa sanya ci gaban a farko a dukkan lamuran sa, tare da bukatar sauran jihohin Najeriya su yi koyi da Kano, musamman yadda gwamnatin ke ware kashi 30 cikin 100 na kasafin kuɗinta a kowace shekara ga fannin ilimi.
Da yake karɓar kyaututtukan a madadin Gwamna Abba Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi na biyu, ya ce gwamnatin ta samu nasarori da dama a fannin ilimi cikin shekaru uku, ciki har da ayyana dokar ta-baci a bangaren, gyaran makarantu, samar da kayan koyo da koyarwa da ruwan sha.
Mai Martaba Sarkin ya ce yunƙurin da ake ci gaba da yi a fannin ilimi ya taimaka wajen ɗaga martabar Kano, har ta zama jiha mafi ƙwazo a jarabawar manyan makarantun sakandare ta NECO a tsakanin jihohin Najeriya a shekarar 2025.
