Tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo, ya yi gargaɗin cewa ƙasar nan ba za ta iya samun ci gaba mai ma’ana ba muddin cin hanci da rashawa na ci gaba da yaɗuwa a tsakanin al’umma da hukumomin gwamnati.
Obasanjo ya bayyana hakan ne a ranar Litinin, yayin gabatar da wani littafi mai suna Unexplained Wealth in Nigeria: Law, Prosecution and the Recovery of Illicit Assets, wanda lauya kuma malami a Jami’ar Legas, Dr. Wahab Shittu, SAN, ya rubuta, taron ya samu halartar manyan jami’an gwamnati, masana shari’a da sauran masu ruwa da tsaki.
Tsohon shugaban ya bayyana cin hanci da rashawa a matsayin ɗaya daga cikin manyan abubuwan da ke kawo cikas ga ci gaban ƙasa, yana mai cewa ba za m’a iya haɗa ci gaba da cin hanci da rashawa a wuri guda ba, ya kuma jaddada cewa talakawa ne suka fi shan wahala a cikin al’ummar da cin hanci da rashawa ya yi katutu, domin hakan na ƙara jefa su cikin fatara.
Obasanjo ya kuma bayyana yadda aka fuskanci turjiya wajen samar da dokar da ta kafa hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta kasa, ICPC, a lokacin mulkinsa, ya ce wasu ’yan majalisar dokoki sun gaya masa cewa idan suka amince da dokar a yadda ya gabatar da ita, da yawa daga cikinsu za su iya fuskantar ɗauri a gidan yari, ya ce hakan ya sa aka shafe kusan watanni 18 ana takaddama kan dokar kafin daga bisani aka amince da ita.
Ya ƙara da cewa gwamnatinsa ta kafa hukumar EFCC a matsayin wani mataki na ƙarfafa yaƙi da laifukan kuɗi da cin hanci da rashawa, Obasanjo ya yi kira da a ci gaba da ƙarfafa hukumomin yaƙi da rashawa, tabbatar da bin doka da kuma aiwatar da sauye-sauyen da za su taimaka wajen dawo da kadarorin da aka wawure, yana mai cewa yaƙi da cin hanci da rashawa na buƙatar jajircewa da ingantattun hukumomi.
