Dan wasan gaba na Najeriya Victor Osimhen, ya cimma yarjejeniya da ƙungiyar Manchester United domin komawa kungiyar lokacin bazara, a cewar wani ɗan jarida daga Turkiyya, Serdar Çelikler.
Osimhen wanda yanzu haka yana Galatasaray a matsayin aro daga Napoli, ance yana cikin koshin lafiya, inda ya jefa kwallaye 29 tare da taimakawa a jefa kwallo 6 a wasanni 34.
Manchester United dai na neman sabon ɗan wasan gaba, saboda rashin kokarin Rasmus Hoylund, wanda ya ci kwallaye uku kacal a gasar Premier League.
Sabon koci Ruben Amorim yana fatan sallamar Hoylund daga kungiyar nan gaba kadan.
Kodayake an riga an amince da sharuddan Osimhen, har yanzu ana ci gaba da tattaunawa tsakanin United da Napoli game da kuɗin sayen dan wasan. Napoli na iya saukaka farashin da ke kwantiragin Osimhen na €75m.
Rahotanni sun ce Manchester United tayi masa tayin albashin £660,000 a mako — wanda zai mayar dashi dan wasan da yafi kowanne daukar albashi a kungiyar.
