Ministan Kuɗi, Wale Edun, ya ce Gwamnatin Tarayya ta ƙuduri aniyar rage yawan ciyo bashi yayin da take daɗa ƙoƙarin jawo masu zuba jari daga ƙasashen waje zuwa Najeriya.
Ministan ya bayyana haka ne a tattaunawarsa da manema labarai a gefen taron Tattalin Arziki na Duniya (WEF) da aka gudanar a Davos, Switzerland, a ranar Talata.
- Gwamnatin tarayya ta yi gargadi kan kulla yarjejeniyar sulhu da ’yan bindiga
- Muna na ci gaba da fito da sabbin hanyoyi magance tsaro-Tinubu
Ya ce koda yake gibin kasafin kuɗin Najeriya ya ƙaru a rubuce bayan amincewar Majalisar Dokoki, yanzu gwamnati ta mayar da hankali kan daidaita harkokin kuɗi bayan aiwatar da muhimman sauye-sauyen tattalin arziki.
A cewar ministan, halartar Najeriya a taron na Davos na nufin nuna sabuwar daidaituwar da tattalin arzikin ƙasar ya samu da kuma jan hankalin masu zuba jari.
Rahotanni sun bayyana cewa ya zuwa tsakiyar shekarar da ta gabata, basukan da ake bin Najeriya ya haura Naira tiriliyan 152, bisa bayanan Ofishin Kula da Basussuka na Ƙasa (DMO).
