Majalisar Dattawa ta koma zaman majalisa a yau, Talata, 15 ga Satumba, bayan shafe kusan makonni shida tana hutun shekara.
Sanatocin sun koma ne a daidai lokacin da zaben 2027 ke kara daukar hankali, bayan hukumar zabe ta INEC ta fitar da jerin sunayen ’yan takarar majalisar dattawa.
Rahoton jaridar The Guardian ya nuna cewa jam’iyyun APC, ADC, NDC da PDP sun shiga gasar neman kujerun majalisar dattawa 109 da za a fafata a zaben shekarar 2027.
Jerin sunayen na INEC ya kuma nuna cewa akalla sanatoci 52 da ke kan kujerunsu a yanzu ba za su koma majalisar ta 11 ba, saboda dalilai daban-daban da suka shafi takara da sauya jam’iyya ko rashin tsayawa takara.
A wasu jihohi kuma, an samu sauye-sauyen yayin da ’yan majalisar wakilai da wasu tsofaffin ’yan majalisa suka koma wasu sabbin jam’iyyu.
Dawowar majalisar na nufin sanatoci za su koma duba muhimman kudurori da dokoki, yayin da kuma za su kara mayar da hankali kan siyasar zaben 2027 da ayyukan mazabunsu
