Saurari premier Radio
22.5 C
Kano
Saturday, September 21, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiPDP ta ki sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya a zaben gwamnan...

PDP ta ki sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya a zaben gwamnan jihar Edo

Date:

Jam’iyyar PDP ta ki sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya a zaben gwamnan jihar Edo da aka shirya gudanarwa a ranar 21 ga watan Satumba.

Tsohon shugaban kasa Abdulsalami Abubakar ne ya bayyana hakan a Alhamis din nan a wajen taro rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya a Benin, babban birnin jihar Edo.

A cewarsa, PDP ta ce za ta sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya ne kawai idan an cika wasu sharudda.
Ya kara da cewa a jiya laraba ya  gana da gwamnan jihar wanda ya tabbatar masa da cewa  PDP ba za ta sanya hannu kan wannan yarjejeniyar zaman lafiya ba, wanda ya tabbatar da cewa idan an cika wadannan sharudda za su zo Abuja su sa hannu.

Duk da cewa jam’iyyar PDP da dan takararta na zaben Asue Ighodalo, ba su sanya hannu ba, amma wasu jam’iyyun da ‘yan takararsu sun sanya hannu, wanda  suka hada da jam’iyyar APC da dan takararta, Monday Okpebholo da dan takarar jam’iyyar LP  Olumide Akpata.

Latest stories

Related stories