
Ma’aikatar Shari’a da haɗin gwiwar Hukumar Wayar Da Kai Ta Ƙasa (NOA) sun ƙaddamar da gagamin wayar da kan jama’a kan laifukan da ake aikatawa a intanet (cybercrime) a faɗin ƙasar nan.
An kaddamar da gangamin ne na Cybercrime Awareness Walk na 2025 a Babban Birnin Tarayya Abuja, a ranar Litinin.
Hukumomin biyu sun buƙaci jama’a, musamman matasa da su kasance masu lura da amfani da fasahar zamani cikin gaskiya da aminci.
Barista Tessy Nnalue da ta wakilci Daraktan Hukumar NOA, ta tabbatar da cewa hukumar za ta ci gaba da gangamin a rediyo, da talabijin, da fassara shi a harsuna daban-daban na kasa da kuma wuraren tarukan al’umma.
Wano babban jami’I daga ofishin Babba Antoni Janar na kasa Muhammad Abubakar Babadoko, ya ce wannan yunƙuri yana daga cikin dabarun gwamnati na ƙarfafa martani kan ƙaruwar laifukan yanar gizo.
Ya kuma ce, gangamin zai kai ga makarantu, kasuwanni, da a dukkan sassan Najeriya.
Sannan ya gargaɗi matasa da su yi amfani da basirarsu wajen ƙirƙire-ƙirƙire da kasuwanci, ba wajen laifukan yanar gizo kamar zamba, da satar bayanai, da cin zarafi ta intanet ba.