Jam’iyyar adawa ta ADC ta ce, iƙirarin gwamnati cewa matakan Shugaba Bola Ahmed Tinubu ne suka kawo sauƙin farashin kayan abinci ba gaskiya ba ne.
Jam’iyyar ta zargi gwamnati da yaudarar ‘yan ƙasa da labarin karya, tana mai cewa abin da ya kawo sauƙin abinci a kasuwa ba ƙoƙarin manufofin gwamnati ba ne.
Kakakin jam’iyyar, Faisal Kabiru, ya ce farashin kayan noman gida ya faɗi ne saboda tsoro da rashin daidaito a kasuwa, ba wai saboda wata nasarar gwamnati ba.
Ya ƙara da cewa manoma da dama yanzu ba su da jarin da za su ci gaba da noma saboda rage farashin kayan da suka noma.
Sai dai gwamnatin Tinubu ta mayar da martani, tana cewa jam’iyyar ADC kawai tana adawa ne da nasarorin da gwamnati ke samu.
Hadimin shugaban kasa, Abdulaziz Abdulaziz, ya ce: “Da farko ‘yan adawa suna ƙorafi cewa abinci ya yi tsada. Yanzu da gwamnati ta ɗauki matakai don rage tsada, sai kuma suke kuka.”
