Ƙungiyar Ƙwadago ta Ƙasa (NLC) ta bayyana cewa za ta gudanar da zanga-zangar ƙasa baki ɗaya a ranar 17 ga Disamba, 2025, domin nuna damuwarta kan taɓarɓarewar tsaro.
Wannan sanarwa ta fito ne daga saƙon da NLC ta aikawa dukkanin majalisun jihohi a ranar 10 ga Disamba, bayan taron NEC da ta gudanar a ranar 4 ga watan.
Kungiyar ta nuna baƙin ciki kan ƙaruwar hare-haren ƴan daba da satar mutane da ke ci gaba da addabar al’umma.
- NLC Ta Shirya Zanga-Zanga a Ranar 17 Ga Disamba
- NLC Ta Dakatar da Zanga-Zanga Kan Karin Kudin Kira Da Data
- Ƙungiyar NUPENG ta dakatar da shiga yajin aiki
NLC ta mayar da hankali musamman kan sace ɗalibai mata a wata makarantar kwana da ke Jihar Kebbi a ranar 17 ga Nuwamba, inda ta bayyana mamaki cewa an janye jami’an tsaro daga makarantar kafin harin.
Ta ce wannan lamari ne mummunan kuma abin takaici da ya kamata a bincike shi sosai tare da gurfanar da duk masu hannu a ciki. Ƙungiyar ta zargi gwamnati da gaza ɗaukar matakan da suka dace wajen kare rayukan ɗalibai a makarantu.
Sanarwar ta ƙara da cewa an umarci dukkan rassan NLC da ƙungiyoyin ƙwadago da su shirya cikakke domin zanga-zangar.
