Shugaban rundunar sojin Nijar ya zargi Faransa, Benin da Côte d’Ivoire da laifin kai hari kan sansanin soja a filin jirgin saman kasa da kasa na Niamey, tare da gode wa sojoji da abokan hulɗa na Rasha saboda daƙile harin.
Wasu da ake zargin ‘yan ta’adda ne suka kai harin bayan ƙarfe 12 na dare a ranar Alhamis, inda mazauna yankin suka ba da rahoton harbe-harbe da fashewar abubuwa har zuwa lokacin aka samu kwanciyar hankali kimanin awa daya bayan faruwar lamarin.
Nijar, wadda ta sha fama da tashin hankali na ta’addanci, na karkashin jagorancin Janar Abdourahamane Tiani tun bayan juyin mulkin da ya kifar da tsohon Shugaban Ƙasa Mohamed Bazoum a watan Yulin 2023.
Babu wata kungiyar ‘yanta’adda da ta dauki alhakin kai harin zuwa yanzu.
- Jamhuriyar Nijar ta yi Karin albashin ma’aikata zuwa N108
- Birtaniya, Faransa da Canada Sun Yi Allah-Wadai da sabbin Hare-haren Isra’ila a Gaza
An dawo da ayyukan tsaro kamar yadda aka saba a filin jirgin saman Diori Hamani, wanda ke da sansanin sojojin sama kuma yana da nisan kilomita 10 daga Fadar Shugaban Ƙasa.
Ma’aikatar tsaron Nijar ta ce an jikkata sojoji hudu kuma an kashe maharan 20, inda gidan talabijin na gwamnati ya ce wani dan kasar Faransa na cikin su.
Danganta tsakanin gwamnatin Nijar da tsohuwar kasar da ta yi mata mulkin mallaka ta yi tsami, kuma tana yawan zargin ta, da ma makaciyarta Benin da yunkurin rikita harkokin siyasar cikin gidanta, zargin da dukkan kasashen biyu suka musanta.
