Ahmad Hamisu Gwale
Hukumar kwallon kafa ta kasa NFF ta gabatar da Éric Sékou Chelle a matsayin babban horar da tawagar Najeriya Super Eagles.
Bikin gabatar da Éric Sékou Chelle ya gudana a yau Litinin a dakin taro na filin wasa na MKO Abiola da ke birnin tarayya Abuja.
Shugaban hukumar wasanni NSC Malam Shehu Dikko, da shugaban hukumar kwallon kafa ta kasa NFF, Alhaji Ibrahim Gusau, da sauran manyan baki sun halarci bikin.
Tun a makon da ya gabata wani kwamitin tsare-tsare na hukumar kwallon kafa ta kasa NFF ya amince da nadin Chelle domin jagorantar Super Eagles.
Kawo yanzu haka babban kalubalen Chelle shi ne jagorantar tawagar Super Eagles B a wasannin gasar kwallon kafa ta CHAN da za a fafata a wata mai kamawa a kasashen Kenya, Tanzania da Uganda.
Bayan wannan kuma, Éric Sékou Chelle zai mayar da hankali wajen jagorantar Super Eagles wasannin fagen shiga gasar cin kofin duniya ta shekarar 2026 da Najeriya za tayi da Rwanda da Zimbabwe a watan Mayu.
Kafin karbar aikin horar da Najeriya Éric Sékou Chelle ya koyar da MC Oran ta kasar Algeria, tun daga shekarar 1989.