Yayin da ake fatan kawo ƙarshen yaƙin Isra’ila a Gaza, firaministan ƙasar Benjamin Netanyahu, ya umarci sojoji da su ci gaba da luguden wuta kan Falasɗinawa a Gaza.
Wannan na zuwa ne bayan da Firaministan Benjamin Netanyahu ya yi zargin cewa Hamas ta karya yarjejeniyar tsagaita wutar da aka cimma a Masar.
Sai dai hukumomi a Gaza sun zargi gwamnatin ta Yahudu da karya ƙa’idojin yarjejeniyar har guda 125, tun daga lokacin da ta fara aiki a ranar 10 ga Oktoba, ciki har da kashe Falasɗinawa 94.
A halin da ake ciki, rahotanni na cewa, an kai hari tsakiyar Gaza, amma babu tabbas ko za a faɗaɗa hare-hare zuwa wasu yankunan.
Duk da cewa an cimma yarjejeniyar tsagaita wuta, bayanai sun ce a ranar Talatar nan Isra’ila ta kai mabanbantan hare-hare guda uku a zirin Gaza.
Guda daga cikin mambobin hamas, Suhail al-Hindi ya bayyana cewa, ƙungiyar na fuskantar matsaloli yayin da take fafutukar gano gawarwakin mutanen da aka kama, yana me bayyana buƙatar kayayyakin aikin tono, la’akari da irin ɓarnar da Isra’ila ta yiwa yankin, wanda ya ce ya danne mutane da dama.
