Cibiyar kula da cututtuka da rigakafin su ta kasa (ncdc) ta gargadi al’umma kan barkewar wata sabuwar cuta mai suna chikungunya a wasu ƙasashen duniya.
Cutar wacce hukumomin lafiya ke kira da chikungunya tana faruwa ne sakamakon ƙwayar cuta da sauro nau’in aedes aegypti da aedes albopictus ke yadawa, waɗanda ke cizon mutum da sassafe da kuma yamma.
Alamomin cutar sun haɗa da zazzabi, ciwon gwiwa da ciwon kai, amai, gajiya, da kuma ƙurajen fata.
A wata sanarwa da aka wallafa a shafinta na Internet a ranar juma’a, hukumar ta ce fiye da mutum 240,000 suka kamu da cutar, yayin da mutane 90 suka mutu a bana a ƙasashe akalla 16, inda ƙasar Chana kaɗai ta tabbatar da kusan mutum 5,000 sun kamu da ita tun farkon watan Yulin shekarar da muke ciki.
Duk da cewa Najeriya ba ta samu wani tabbacin bullar cutar ba, NCDC ta yi gargadin cewa yanayin muhalli musamman a jihohin da ambaliyar ruwa ta shafa na iya ba da damar yaduwar cutar.
Cibiyar ta shawarci jama’a da su kare kansu daga cizon sauro ta hanyar yin barci a gidan sauro, sanya kaya masu rufe jiki, amfani da magungunan fitar da sauro, da kuma kawar da ruwan da ke tsaye a kusa da gidaje.
Ta ƙara da cewa tana haɗa kai da hukumomin lafiya domin ƙarfafa binciken sauro, tallafawa ma’aikatan lafiya wajen gano cutar da wuri, tare da wayar da kan jama’a kan tsafta da kariya.
