Gwamnatin Najeriya ta ce tana cikin tsananin ɓacin rai kan kisan ƴan ƙasar ta biyu, Bishop Taiwo Michael Fakunle da James Uchechukwu Nwankwo, a cikin mako guda a biranen Johannesburg da Cape Town na ƙasar Afrika ta Kudu.
A cewar Ma’aikatar Harkokin Wajen Najeriya, Bishop Fakunle ya mutu ne bayan da aka kai masa hari a gidansa, yayin da Nwankwo ya rasu sakamakon tsananin azabar bincike a hannun jami’an ƴan sandan Afrika ta Kudu.
A wata sanarwa da mai magana da yawun ma’aikatar, Oluwafemi Adeniyi, ya fitar, Najeriya ta ce lamarin ya ƙara nuna ƙyamar baƙi da ake yi da kai musu hare‑hare musamman ƴan Afrika, a ƙasar, kuma lamarin da ya faru ya sake nuna gazawar hukumomin tsaro wajen kare rayukan baƙi.
Sanarwar ta yi kira ga hukumomin Afrika ta Kudu da su gudanar da bincike mai zurfi kuma cikin gaggawa domin gano masu laifi da gurfanar da su.
Najeriya ta ce ta gabatar da batun ƙyamar baƙi ga shugabannin ECOWAS da AU, kuma tana nazarin ƙarin matakan diflomasiyya domin kare ƴan ƙasar ta a Afrika ta Kudun
